1 Sarakuna 7:23 - Littafi Mai Tsarki23 Huram kuma ya yi kewayayyiyar babbar kwatarniya ta zubi da tagulla. Faɗinta kamu goma ne, tsayinta kuwa kamu biyar, da'irarta kuma kamu talatin ne. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202023 Sai Huram ya yi wani ƙaton kwano na ƙarfen tagulla, da ya kira Teku. Zurfin kwanon nan kamu bakwai da rabi, fāɗinsa kamu goma sha biyar, da’irarsa kuma kamu talatin ne. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sarki Ahaz ya umarci Uriya firist cewa, “Sai ka miƙa hadaya ta ƙonawa ta safe, da hadaya ta gari ta maraice, da hadaya ta ƙonawa ta sarki, da hadayarsa ta gari, da hadaya ta ƙonawa ta dukan jama'ar ƙasar, da hadayarsu ta gari, da hadayarsu ta sha, ka yayyafa dukan jinin hadaya ta ƙonawa, da dukan jinin hadayu a bisa babban bagaden. Amma bagaden tagulla zai zama nawa don yin ibada.”