Sulemanu ya gama kai da Fir'auna, Sarkin Masar, ta wurin aure, domin ya auri 'yar Fir'auna, ya kawo ta birnin Dawuda kafin ya gama ginin gidan kansa, da Haikalin Ubangiji, da garun Urushalima.
A shekara ta goma sha ɗaya ta sarautar Sulemanu a watan Bul, wato watan takwas, aka gama ginin Haikalin, daidai yadda aka zayyana fasalinsa. Sulemanu ya yi shekara bakwai yana ginin Haikalin.