4 Ya yi wa Haikalin tagogi, suna da fāɗi daga ciki fiye da waje.
4 Ya yi tagogin da suka fi fāɗi daga ciki fiye da waje a haikalin.
Akwai tagogi masu murfi da yake fuskantar ɗakunan 'yan tsaro da kuma ginshikansu waɗanda suke wajen ƙofa a kewaye, haka nan kuma shirayin. Daga ciki kuma akwai tagogi a kewaye. A kowane ginshiƙi an zana siffar itatuwan dabino.
Akwai tagogi masu gagara badau a kowane gefen ɗakin. An kuma zāna bangon da siffar itatuwan dabino.
Ƙaunataccena kamar barewa yake, Kamar sagarin kishimi. Ga shi can, yana tsaye a bayan katangarmu. Yana leƙe ta tagogi, Yana kallona ta cikin asabari.
Tsawon shirayin da yake a gaban Haikalin kamu ashirin ne, wato daidai da fāɗin Haikalin. Fāɗinsa kuma daga gaban Haikalin kamu goma ne.
Aka kuma yi tagogi masu sandunan ƙarfe, jeri uku, kowace taga tana daura da 'yar'uwarta, har jeri uku.