Sa'an nan Hiram ya aika wurin Sulemanu, ya ce, “Na ji saƙonka da ka aiko mini, a shirye nake in yi maka dukan abin da kake bukata a kan katakan itacen al'ul, da na fir.
Sai Dawuda da Isra'ilawa duka suka yi rawa sosai don farin ciki a gaban Ubangiji. Aka yi ta raira waƙoƙi, ana kaɗa molaye, da garayu, da goge, da kacakaura, da kuge.