1 Sarakuna 6:3 - Littafi Mai Tsarki3 Tsawon shirayin da yake a gaban Haikalin kamu ashirin ne, wato daidai da fāɗin Haikalin. Fāɗinsa kuma daga gaban Haikalin kamu goma ne. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 Shirayin da yake a gaban ainihin zauren haikalin, ya ƙara faɗin haikalin da kamu ashirin, ya kuma nausa daga gaban haikalin kamu goma. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ya kuma auna tsawon ginin da yake fuskantar farfajiyar da take wajen yamma da hanyar fita, kamu ɗari ne. Cikin Haikalin, da ɗaki na can ciki, da shirayi, dukansu uku suna da tagogi masu gagara badau. An manne bangon Haikalin da yake fuskantar shirayin da katako, tun daga ƙasa har zuwa tagogi. [Tagogin kuma an rufe su.]