Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 6:29 - Littafi Mai Tsarki

29 Ya zana siffofin kerubobi, da na itatuwan dabino, da na furanni a dukan bangon Haikalin, wato bango na Wuri Mai Tsarki da Wuri Mafi Tsarki na can ciki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

29 A bangaye kewaye da haikali, a ɗakuna ciki da waje, ya zāzzāna kerubobi, itatuwan dabino, da furanni buɗaɗɗu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 6:29
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai ya zazzāna siffofin kerubobi, da na itatuwan dabino, da na furanni a kan ƙofofi duka biyu, sa'an nan ya dalaye duk ƙofofin da zinariya.


Bayan wannan na duba, ga wani ƙasaitaccen taro, wanda ya fi gaban ƙirge, daga kowace al'umma, da kabila, da jama'a, da harshe, suna a tsaitsaye a gaban kursiyin, a gaban Ɗan Ragon kuma, a saye da fararen riguna, da gazarin dabino a hannunsu,


An yi wannan ne kuwa domin a yanzu a sanar da hikimar Allah iri iri ga manyan mala'iku da masu iko a samaniya, ta hanyar Ikkilisiya.


Ku yabe shi dukanku mala'ikunsa, Ku yabe shi, ku dukan rundunansa na sama!


Ku yabi Ubangiji, ku ƙarfafa, ku manyan mala'iku, Ku da kuke biyayya da umarnansa, Kuna kasa kunne ga maganarsa!


Sai ya yi labule mai launin shuɗi, da shunayya, da garura, da lilin mai kyau, sa'an nan ya zana siffofin kerubobin a jikin labulen.


Katakan itacen al'ul na cikin Haikalin, an yi musu zāne mai fasalin gora da na furanni buɗaɗɗu. An rufe bangon daga ciki duka da itacen al'ul, har ba a ganin duwatsun ginin.


Sai dukan mutane masu gwaninta daga cikin ma'aikatan, suka yi alfarwa da labule goma. An yi labulen da lallausan zaren lilin na shuɗi, da shunayya, da mulufi. Aka yi wa labulen zānen kerubobi na gwaninta.


Har daɓen ƙasa, ya dalaye shi da zinariya.


Ya kuma shafe Haikalin duk da ginshiƙansa, da bakin ƙofofinsa, da bangayensa, da ƙyamarensa da zinariya, ya kuma zana siffofin kerubobi a jikin bangaye.


Da gaturansu da gudumarsu, Sun ragargaje ƙyamaren da aka yi da katako.


Akwai tagogi masu murfi da yake fuskantar ɗakunan 'yan tsaro da kuma ginshikansu waɗanda suke wajen ƙofa a kewaye, haka nan kuma shirayin. Daga ciki kuma akwai tagogi a kewaye. A kowane ginshiƙi an zana siffar itatuwan dabino.


“Alfarwar kanta, za ku yi ta da labule goma na lilin mai laushi ninki biyu, da ulu mai launi shuɗi, da launi shunayya da launi ja. Waɗannan labule za a yi musu zānen siffofin kerubobi, aikin gwani.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ