28 Ya dalaye kerubobin da zinariya.
Ya sa kerubobin daura da juna a can cikin Haikali domin fikafikan su taɓi juna a tsakiya kowane ɗayan kuma ya taɓi bango.
Ya zana siffofin kerubobi, da na itatuwan dabino, da na furanni a dukan bangon Haikalin, wato bango na Wuri Mai Tsarki da Wuri Mafi Tsarki na can ciki.