A shekara ta goma sha ɗaya ta sarautar Sulemanu a watan Bul, wato watan takwas, aka gama ginin Haikalin, daidai yadda aka zayyana fasalinsa. Sulemanu ya yi shekara bakwai yana ginin Haikalin.
Haka sarki Sulemanu ya gama dukan aikin Haikalin Ubangiji. Sai ya kawo abubuwan da tsohonsa Dawuda ya keɓe, wato azurfa, da zinariya, da kayayyakin aiki, ya ajiye su cikin taskokin Haikalin Ubangiji.
Sau uku a shekara Sulemanu yakan miƙa hadayu na ƙonawa, da na salama, da hadayar turare, a kan bagaden da ya gina wa Ubangiji. Ta haka aka gama ginin Haikali.