Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 6:1 - Littafi Mai Tsarki

1 A shekara ta arbaminya da tamanin bayan fitowar mutanen Isra'ila daga ƙasar Masar, a shekara ta huɗu ta sarautar Sulemanu, Sarkin Isra'ila, a watan biyu, wato watan Zib, sai Sulemanu ya fara gina Haikalin Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 A shekara ta ɗari huɗu da tamani bayan fitowar Isra’ilawa daga Masar, a shekara ta huɗu ta mulkin Solomon a bisa Isra’ila, a watan Zif, wata na biyu, Solomon ya fara gina haikalin Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 6:1
26 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ku kuma, kamar rayayyun duwatsu, bari a gina gida mai ruhu da ku, domin ku zama tsattsarkar ƙungiyar firistoci, da nufin ku miƙa hadayu na ruhu, abin karɓa ga Allah, ta wurin Yesu Almasihu,


Ka kuma ba ɗana Sulemanu cikakkiyar zuciya, har da zai kiyaye umarnanka, da shaidunka, da dokokinka, domin ya aikata su duka, ya kuma gina Haikali wanda na riga na yi tanadi dominsa.”


A shekara ta huɗu ta sarautar Sulemanu aka kafa harsashin ginin Haikalin Ubangiji a watan biyu, wato watan Zib.


Yana ta jiran birnin nan mai tushe, wanda mai fasalta shi, mai gina shi kuma, Allah ne.


Amma Almasihu ya riga ya zo, yana babban firist na kyawawan abubuwan da suke akwai. Masujadar da yake hidima a ciki mafi ɗaukaka ce, mafi kammala kuwa (wadda ba yin mutum ba ce, wato, ba ta wannan halittacciyar duniya ba ce).


kuna kafaffu, kuna ginuwa a cikinsa, kuna tsayawa da bangaskiya gaba gaba, daidai yadda aka koya muku, kuna gode wa Allah a koyaushe.


Wace yarjejeniya ce take a tsakanin Haikalin Allah da gumaka? Domin mu haikali ne na Allah Rayayye. Yadda Allah ya ce, “Zan zauna tare da su, in yi yawo a tsakaninsu, Zan kuma kasance Allahnsu, Su kuma su kasance jama'ata.


Ashe, ba ku sani ba, jikinku Haikali ne na Ruhu Mai Tsarki wanda yake a zuciyarku, wanda kuka kuma samu a gun Allah? Ai, ku ba mallakar kanku ba ne.


“Waɗanda yake nesa za su zo su gina Haikalin Ubangiji. Za ku kuwa sani Ubangiji Mai Runduna ya aiko ni wurinku. Wannan zai faru idan kun yi biyayya sosai da muryar Ubangiji Allahnku.”


Shekara ɗari uku Isra'ilawa suka yi zamansu a Heshbon da ƙauyukanta, da Arower da ƙauyukanta, da dukan biranen da suke a gefen Kogin Arnon, me ya sa ba ka ƙwace su tun a wancan lokaci ba?


A rana ta fari ga wata na biyu a shekara ta biyu bayan da Isra'ilawa suka bar Masar, Ubangiji ya yi magana da Musa a cikin alfarwa ta sujada a jejin Sinai. Ya ce,


Ya kuma hallaka al'umma bakwai a ƙasar Kan'ana, sai ya raba musu ƙasar tasu gādo, suka zauna har shekara arbaminya da hamsin.


Haikalin da sarki Sulemanu ya gina wa Ubangiji, tsawonsa kamu sittin, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kamu talatin ne.


da Azariya wanda ya yi hidimar firist a Haikalin da Sulemanu ya gina a Urushalima.


To, sai suka ce mana, ‘Mu bayin Allah ne wanda yake da sama da ƙasa, muna sāke gina Haikalin da wani babban sarki na Isra'ila ya gina tun shekaru da yawa da suka wuce.


A can ya gina Haikalinsa, Kamar wurin zamansa a Sama. Ya kafa shi da ƙarfi kamar duniya, Tabbatacce a kowane lokaci.


Ku haura zuwa kan tuddai, ku kawo itace don ku gina Haikalina, in ji daɗinsa, a kuma ɗaukaka ni.


A ranar da shekara arbaminya da talatin ɗin nan suka cika, a ran nan ne dukan rundunar Ubangiji suka fita daga ƙasar Masar.


A wannan rana ce Ubangiji ya fitar da Isra'ilawa runduna runduna daga ƙasar Masar.


Ga awon harsashin da Sulemanu ya kafa domin ginin Haikalin Ubangiji. Tsawonsa bisa ga tsohon magwajin, kamu sittin ne, fāɗin kuwa kamu ashirin.


Sai ya kai ni cikin Haikalin, sa'an nan ya auna ginshiƙai. Fāɗin ginshiƙan kamu shida ne a kowane gefe.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ