1 Sarakuna 4:8 - Littafi Mai Tsarki8-19 Waɗannan su ne hakimai, da kuma lardunan da suke aiki. Ben-hur yana a ƙasar tudu ta Ifraimu. Ben-deker shi ne mai lura da biranen Makaz, da Shalim, da Bet-shemesh, da Elon-bet-hanan. Ben-hesed shi ne mai lura da Arubot, da Soko, da dukan ƙasar Hefer. Ben-abinadab shi ne mai lura da dukan jihar Dor, ya auri Tafat 'yar Sulemanu. Ba'ana ɗan Ahilud shi ne mai lura da biranen Ta'anak da Magiddo, da dukan jihar Bet-sheyan, kusa da garin Zaretan, kudu da garin Yezreyel, har zuwa birnin Abel mehola da birnin Yokmeyam. Ben-geber shi ne mai fura da birnin Ramot-gileyad, da ƙauyukan Yayir da Manassa, waɗanda suke a Gileyad, da kuma yankin Argob, wanda yake a Bashan, duka dai akwai manyan garuruwa sittin masu garu da ƙyamare na tagulla. Abinadab ɗan Iddo shi ne mai lura da birnin Mahanayim. Ahimawaz shi ne mai lura da Naftali, ya auri Basemat 'yar Sulemanu. Ba'ana ɗan Hushai shi ne mai lura da Ashiru da garin Beyalot. Jehoshafat ɗan Faruwa shi ne mai lura da Issaka. Shimai ɗan Ila shi ne mai lura da ƙasar Biliyaminu. Geber ɗan Uri shi ne mai lura da jihar Gileyad wadda Sihon Sarkin Amoriyawa, da Og Sarkin Bashan, suka mallaka. Bayan waɗannan sha biyu akwai hakimi ɗaya da yake kan ƙasar Yahuza. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20208 Ga sunayensu, Ben-Hur, shi ne a ƙasar tudun Efraim; အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |