Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 4:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Sulemanu kuma ya naɗa mutum goma sha biyu a lardunan Isra'ila. Su ne za su tanaji abinci daga lardunansu domin sarki da iyalinsa. Kowane hakimi yakan kawo abinci wata guda a shekara.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Solomon yana da gwamnoni yankuna goma sha biyu a bisa dukan Isra’ila, waɗanda suke tanaji abinci domin sarki da kuma gidan sarauta. Kowanne yakan tanada abinci na wata ɗaya a shekara.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 4:7
6 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Waɗannan su ne hakimai, da kuma lardunan da suke aiki. Ben-hur yana a ƙasar tudu ta Ifraimu. Ben-deker shi ne mai lura da biranen Makaz, da Shalim, da Bet-shemesh, da Elon-bet-hanan. Ben-hesed shi ne mai lura da Arubot, da Soko, da dukan ƙasar Hefer. Ben-abinadab shi ne mai lura da dukan jihar Dor, ya auri Tafat 'yar Sulemanu. Ba'ana ɗan Ahilud shi ne mai lura da biranen Ta'anak da Magiddo, da dukan jihar Bet-sheyan, kusa da garin Zaretan, kudu da garin Yezreyel, har zuwa birnin Abel mehola da birnin Yokmeyam. Ben-geber shi ne mai fura da birnin Ramot-gileyad, da ƙauyukan Yayir da Manassa, waɗanda suke a Gileyad, da kuma yankin Argob, wanda yake a Bashan, duka dai akwai manyan garuruwa sittin masu garu da ƙyamare na tagulla. Abinadab ɗan Iddo shi ne mai lura da birnin Mahanayim. Ahimawaz shi ne mai lura da Naftali, ya auri Basemat 'yar Sulemanu. Ba'ana ɗan Hushai shi ne mai lura da Ashiru da garin Beyalot. Jehoshafat ɗan Faruwa shi ne mai lura da Issaka. Shimai ɗan Ila shi ne mai lura da ƙasar Biliyaminu. Geber ɗan Uri shi ne mai lura da jihar Gileyad wadda Sihon Sarkin Amoriyawa, da Og Sarkin Bashan, suka mallaka. Bayan waɗannan sha biyu akwai hakimi ɗaya da yake kan ƙasar Yahuza.


“Tsohonka ya nawaita mana, yanzu sai ka rage mana wahalar aikin tsohonka da nawayarsa a kanmu, mu kuwa za mu bauta maka.”


Da Hiram ya ji maganar Sulemanu, sai ya yi murna ƙwarai, ya ce, “Yabo ga Ubangiji saboda wannan rana, gama ya ba Dawuda ɗa mai hikima da zai shugabanci wannan babbar jama'a.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ