Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 3:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Ga ni kuwa a tsakiyar jama'arka wadda ka zaɓa, jama'a mai yawa wadda ba ta ƙidayuwa saboda yawansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Bawanka yana nan a cikin mutanen da ka zaɓa, mutane masu girma, waɗanda suka wuce ƙirge, ko a lissafta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 3:8
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Ubangiji ya fito da shi waje ya ce, “Ina so ka dubi sararin sama, ka kuma ƙidaya taurari, in kana iya ƙidaya su.” Sai kuma ya ce masa, “Haka zuriyarka za ta zama.”


Dawuda fa ya ce wa Yowab da sauran shugabannin jama'a, “Ku tafi, ku ƙidaya jama'ar Isra'ila tun daga Biyer-sheba har zuwa Dan, ku kawo mini labari don in san yawansu.”


hakika zan sa maka albarka, zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sama, kamar yashi kuma a gāɓar teku. Zuriyarka za su mallaki ƙofar maƙiyanka,


Zan mai da zuriyarka kamar turɓayar ƙasa, har in mutum ya iya ƙidaya turɓayar ƙasa, to, a iya ƙidaya zuriyarka.


Ya ɗauko shi daga inda yake lura da 'yan raguna. Ya naɗa shi Sarkin Isra'ila, Ya naɗa shi makiyayin jama'ar Allah.


Gama Ubangiji ya yi ƙaƙƙarfan alkawari, ba zai yashe ku ba, gama ya ɗauri aniya ya maishe ku jama'arsa.


Mutanen Yahuza da na Isra'ila suka yi yawa kamar yashi a bakin teku. Suka ci, suka sha, suka yi murna.


Zan dube ku da idon rahama, in sa muku albarka, in riɓaɓɓanya ku. Zan tabbatar muku da alkawarina.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ