Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 3:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Sulemanu ya amsa ya ce, “Kai ne kake nuna ƙauna mai girma a koyaushe ga bawanka Dawuda, tsohona, domin ya yi tafiya a gabanka da aminci, da adalci, da tawali'u. Kai kuwa ka tabbatar masa da wannan ƙauna mai girma, ka kuma ba shi ɗa wanda zai hau gadon sarautarsa a wannan rana.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Solomon ya amsa ya ce, “Ka nuna alheri mai girma ga bawanka, mahaifina Dawuda domin ya yi aminci gare ka da adalci, ya kuma kasance da zuciya mai gaskiya. Ka ci gaba da wannan alheri mai girma gare shi, ka ba shi ɗa don yă zauna a kujerar sarautarsa a wannan rana.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 3:6
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma kai, idan ka yi tafiya a gabana kamar yadda tsohonka, Dawuda, ya yi da aminci, da sahihanci, kana aikata dukan abin da na umarce ka, kana kuma kiyaye dokokina da ka'idodina,


Sa'an nan ya ce, ‘Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na Isra'ila wanda ya sa ɗaya daga cikin zuriyata ya hau gadon sarautata yau, idona kuwa ya gani.’ ”


Za a wadata ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa a yalwace, bayarwar nan kuwa da za ku yi, za ta zama sanadin godiya ga Allah ta wurinmu.


domin Ubangiji ya cika maganar da ya faɗa mini cewa, ‘Idan 'ya'yanka suna lura da hanyarsu, sun yi tafiya a gabana da gaskiya da zuciya ɗaya, da dukan ransu, ba za ka rasa mutum wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba.’


Saboda haka, na dai ga lalle ne in roƙi 'yan'uwan nan su riga ni zuwa a gare ku, su tanada baiwar nan da kuka yi alkawari kafin in zo, domin a same ta a shirye, ba tare da matsawa ba, sai dai kyautar sa kai.


Ka yi mini alheri, ni bawanka, Domin in rayu in yi biyayya da koyarwarka.


Kada ki yi shakka, ya zuciyata, Gama Ubangiji yana yi mini alheri.


Sai dai mutumin da yake biyayya ga Allah da kowane abu, Yana kuwa aikata abin da yake daidai, Wanda yake faɗar gaskiya da zuciya ɗaya,


“Ka tuna da ni yanzu, ya Ubangiji, ina roƙonka, da yadda na yi tafiya a gabanka da aminci, da zuciya ɗaya, na aikata abin da yake mai kyau a gabanka.” Sai ya yi ta rusa kuka.


Ya ce, “Tafi, ka faɗa wa bawana Dawuda, ka ce, in ji Ubangiji, ‘Ɗakin zama za ka gina mini?


Ba haka nake magana da bawana Musa ba, na sa shi ya lura da dukkan jama'ata Isra'ila.


Zan raira waƙa ga Ubangiji, Gama ya kyautata mini.


domin Dawuda ya aikata abu mai kyau a gaban Ubangiji. Bai ƙetare umarnin da Ubangiji ya ba shi ba dukan kwanakin ransa, sai dai a kan Uriya Bahitte.


Idan za ka yi mini biyayya ka kuma kiyaye dokokina, da umarnaina kamar yadda tsohonka Dawuda ya yi, to, zan ba ka tsawon rai.”


Sai Sulemanu ya ce wa Allah, “Ka nuna wa tsohona Dawuda madawwamiyar ƙaunarka, har ka naɗa ni sarki a matsayinsa.


Amma ya amsa mini ya ce, ‘Ubangiji wanda nake tafiya a gabansa zai aiki mala'ikansa tare da kai, ya arzuta hanyarka, za ka kuwa auro wa ɗana mace daga cikin dangina daga gidan mahaifina.


“Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina, Ya sa mini albarka domin ba ni da laifin kome.


Domin haka ya sāka mini bisa ga adalcina, Gama ya sani ba ni da laifi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ