Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 3:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Ubangiji kuwa ya bayyana ga Sulemanu cikin mafarki a Gibeyon da dare, ya ce masa, “Ka roƙi abin da kake so in ba ka.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 A Gibeyon, Ubangiji ya bayyana ga Solomon da dare a mafarki, Allah ya ce, “Ka roƙi abin da kake so in ba ka.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 3:5
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

sai Ubangiji ya sāke bayyana gare shi, kamar yadda ya bayyana gare shi a Gibeyon.


Ya ce, “Ku ji abin da zan faɗa! Idan akwai annabawa a cikinku, nakan bayyana gare su cikin wahayi, in kuma yi magana da su ta cikin mafarki.


Sai ya ce musu, “Me kuke so in yi muku?”


Da suka tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, “Tashi ka ɗauki ɗan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu ƙasar Masar, ka zauna a can sai na faɗa maka, don Hirudus yana shirin binciko ɗan yaron yă hallaka shi.”


Ubangiji kuwa ya yi fushi da Sulemanu, domin zuciyar Sulemanu ta rabu da Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda ya bayyana a gare shi sau biyu,


Ba ku kuka zaɓe ni ba, ni ne na zaɓe ku, na sa ku ku je ku yi 'ya'ya, 'ya'yanku kuma su tabbata, domin kome kuka roƙi Uba da sunana yă ba ku.


Amma bayan mutuwar Hirudus, sai ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki a Masar, ya ce,


Amma tun yana cikin wannan tunani, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana a gare shi a mafarki, ya ce, “Yusufu ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukar Maryamu matarka, domin cikin nan nata daga Ruhu Mai Tsarki ne.


Don haka ina dai gaya muku, kome kuka roƙa da addu'a, ku gaskata cewa samamme ne, za ku kuwa samu.


In kun zauna a cikina, maganata kuma ta zauna a cikinku, za ku roƙi duk abin da kuke so, za a kuwa yi muku.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ