Domin haka ka ba ni hikima ta yi wa jama'arka shari'a, domin in rarrabe tsakanin nagarta da mugunta, gama wane ni in iya mallakar jama'arka mai yawa haka?”
Ya kuma ce masa. “Da yake ka roƙi wannan, ba ka roƙar wa kanka yawan kwanaki, ko wadata ba, ko kuma ran maƙiyanka, amma ka roƙa a ba ka hikima yadda za ka mallaki jama'a,