Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 3:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Sulemanu ya gama kai da Fir'auna, Sarkin Masar, ta wurin aure, domin ya auri 'yar Fir'auna, ya kawo ta birnin Dawuda kafin ya gama ginin gidan kansa, da Haikalin Ubangiji, da garun Urushalima.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Solomon ya haɗa kai da Fir’auna sarkin Masar, ya kuwa auri ’yarsa. Ya kawo ta cikin Birnin Dawuda kafin yă gama ginin fadarsa, da haikalin Ubangiji, da kuma katanga kewaye da Urushalima.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 3:1
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da 'yar Fir'auna matar Sulemanu ta fita birnin Dawuda, zuwa gidan kanta wanda Sulemanu ya gina mata, sa'an nan ya gina birnin Millo.


Sarki Sulemanu ya ƙaunaci baƙin mata. Banda 'yar Fir'auna, Sarkin Masar, ya auri matan Mowabawa, da na Ammonawa, da na Edomawa, da na Sidoniyawa, da na Hittiyawa.


Sulemanu kuwa ya kawo 'yar Fir'auna daga birnin Dawuda zuwa gidan da ya gina mata, gama ya ce, “Matata ba za ta zauna a gidan Dawuda, Sarkin Isra'ilawa ba, saboda duk wuraren da akwatin Ubangiji ya shiga sun tsarkaka.”


A shekara ta arbaminya da tamanin bayan fitowar mutanen Isra'ila daga ƙasar Masar, a shekara ta huɗu ta sarautar Sulemanu, Sarkin Isra'ila, a watan biyu, wato watan Zib, sai Sulemanu ya fara gina Haikalin Ubangiji.


Duk da haka Dawuda ya ci kagarar Sihiyona, wato birnin Dawuda.


To, sai suka ce mana, ‘Mu bayin Allah ne wanda yake da sama da ƙasa, muna sāke gina Haikalin da wani babban sarki na Isra'ila ya gina tun shekaru da yawa da suka wuce.


Yehoshafat ya arzuta, ya kuma sami ɗaukaka sai ya yi ma'amala da Ahab ta wurin aurayya.


Sa'an nan Dawuda ya zauna a kagara, don haka aka kira birnin, birnin Dawuda.


Za mu sake ƙetare umarninka, mu yi aurayya da mutanen da suke yin waɗannan ƙazanta? Ba za ka yi fushi da mu, ka ƙone mu da fushinka har babu ringi ba?


Sa'an nan Dawuda ya rasu, aka binne shi a birnin Urushalima.


Sulemanu ya yi shekara goma sha uku yana gina gidansa kafin ya gama shi duka.


Ya gina gidan da zai zauna a farfajiya na ciki, wajen shirayi. ya kuma gina wa matarsa, 'yar Fir'auna, gida irin wannan.


Sulemanu ya yi shekara ashirin kafin ya gama ginin Haikalin Ubangiji da fādarsa.


'Ya'yansu tsara ta uku, za su iya shiga taron jama'ar Ubangiji.”


Da Sulemanu ya gama ginin Haikalin Ubangiji da na fāda, da dukan abin da ya so ya yi,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ