1 Sarakuna 22:8 - Littafi Mai Tsarki8 Sarkin Isra'ila ya ce wa Yehoshafat, “Da sauran mutum ɗaya wanda za mu iya mu tambaya faɗar Ubangiji, shi ne Mikaiya ɗan Imla, amma ina ƙinsa, gama bai taɓa yin wani annabcin alheri a kaina ba, sai dai na masifa.” Yehoshafat ya ce, “Kada sarki ya faɗi haka.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20208 Sarkin Isra’ila ya amsa wa Yehoshafat, ya ce, “Akwai mutum guda har yanzu wanda ta wurinsa za mu iya nemi nufin Ubangiji, amma na ƙi jininsa domin bai taɓa yin annabci wani abu mai kyau game da ni ba, sai dai mummuna kullum. Shi ne Mikahiya ɗan Imla.” Yehoshafat ya ce, “Kada sarki ya ce haka.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Mai Fansa, Ya ce wa wanda aka raina ƙwarai, Al'ummai suka ƙi shi, Bawa na masu mulki kuma, “Sarakuna za su gan ka a sake, Su kuma miƙe tsaye su ba ka girma, Shugabanni su kuma za su gani, Su rusuna har ƙasa su ba ka girma.” Wannan kuwa zai faru saboda Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya zaɓi bawansa, Ya kuwa cika alkawaransa.