Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 22:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Sa'an nan Sarkin Isra'ila ya tara annabawa ɗari huɗu, ya tambaye su, ya ce, “In tafi in yi yaƙi da Ramot-gileyad, ko kuwa kada in tafi?” Su kuwa suka ce masa, “Ka haura, gama Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Saboda haka sarkin Isra’ila ya tattara annabawa, kamar ɗari huɗu, ya tambaye su, “In kai yaƙi a kan Ramot Gileyad, ko kada in kai?” Suka amsa, “Ka tafi, gama Ubangiji zai ba ka ita a hannunka.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 22:6
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yanzu fa ka aika a tattara mini Isra'ila duka a dutsen Karmel, da annabawan Ba'al, su ɗari huɗu da hamsin, da annabawan Ashtarot kuma, su ɗari huɗu waɗanda Yezebel take kula da su.”


“Kun karya zuciyar adali ta wurin ƙaryarku, ko da yake ni ban karya zuciyarsa ba. Kun ƙarfafa wa mugu gwiwa, don kada ya bar hanyarsa ta mugunta, ya tsira.


Sai aka kama dabbar, da kuma annabin nan na ƙarya tare da ita, wanda ya yi al'ajabai a gabanta, waɗanda da su ne ya yaudari waɗanda suka yarda a yi musu alamar dabbar nan, da kuma waɗanda suka yi wa siffarta sujada. Waɗannan biyu kuwa aka jefa su da ransu a cikin tafkin wuta da ƙibiritu.


Don lokaci zai zo da mutane ba za su jure sahihiyar koyarwa ba, amma saboda kunnensu yana ƙaiƙayi, sai su taro masu koyarwa da za su biya musu muradinsu.


“Ku kula da annabawan ƙarya, waɗanda sukan zo muku da siffar tumaki, amma a zuci kyarketai ne masu ƙāwa.


Annabawa sun yi annabcin ƙarya, Firistoci kuma sun yi mulki da ikon kansu, Mutanena kuwa suna so haka! Amma sa'ad da ƙarshe ya zo, me za ku yi?”


Da Mikaiya ya zo gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Mikaiya, mu haura zuwa Ramot-gileyad mu fāɗa mata da yaƙi, ko in haƙura?” Mikaiya kuwa ya amsa, ya ce, “Ka haura, gama za ka ci nasara, gama za a bashe su a hannunka.”


Da ya zo gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Mikaiya, mu tafi Ramot don yaƙi, ko kuwa kada mu tafi?” Ya amsa masa ya ce, “Ka haura, za ka yi nasara, Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”


Yehoshafat ya ce wa Sarkin Isra'ila, “Ka nemi faɗar Ubangiji tukuna.”


Sarkin Isra'ila da Yehoshafat, Sarkin Yahuza, suna zaune a kujerun sarautarsu, saye da tufafinsu a dandalin ƙofar Samariya. Annabawa kuwa suna annabci a gabansu.


Elisha kuwa ya ce wa Sarkin Isra'ila, “Ina ruwana da kai? Tafi wurin annabawan tsohonka da na tsohuwarka.” Amma Sarkin Isra'ila ya ce masa, “A'a, ai, Ubangiji ya kirawo mu, mu sarakunan nan uku, domin ya bashe mu a hannun Mowabawa.”


Saboda haka, yanzu sai ku kirawo mini dukan annabawan Ba'al, da dukan masu yi masa sujada, da dukan firistocinsa. Kada a manta da wani, gama ina da babbar hadayar da zan miƙa wa Ba'al. Duk wanda bai zo ba, za a kashe shi.” Amma dabara ce Yehu yake yi don ya hallaka waɗanda suke yi wa Ba'al sujada.


Kana tsammani na tasar wa ƙasarka na kuma lalatar da ita ba tare da taimakon Ubangiji ba? Ubangiji da kansa ne ya faɗa mini in tasar wa ƙasarka in lalatar da ita.”


Ya ce musu, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa mutanen nan da suka roƙe ni wai in rage musu nawayar da tsohona ya aza musu?”


Sai Ahab ya aika wa dukan jama'ar Isra'ila, ya tattara annabawa ɗin tare da su a dutsen Karmel.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ