Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 22:52 - Littafi Mai Tsarki

52 Ya yi zunubi a gaban Ubangiji. Ya bi halin tsohonsa da na tsohuwarsa, da na Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra'ila su yi zunubi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

52 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, domin ya yi tafiya a hanyoyin mahaifinsa da na mahaifiyarsa, da kuma a hanyoyin Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila suka yi zunubi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 22:52
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya yi wa Ubangiji zunubi kamar yadda tsohonsa ya yi, ya kuma sa Isra'ila su yi zunubi.


Babu wani kamar Ahab da ya ba da kansa ga aikata mugunta a gaban Ubangiji. Matarsa, Yezebel, ita ce ta zuga shi.


Ga ni nan a tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa, kowa ya ji muryata ya buɗe ƙofar, sai in shiga wurinsa, in ci abinci tare da shi, shi kuma tare da ni.


Ta fita, ta ce wa uwa tata, “Me zan roƙa?” Uwar ta ce, “Kan Yahaya Maibaftisma.”


Ya kuma bi gurbin gidan Ahab, gama tsohuwarsa ita ce mai ba shi shawarar yadda zai aikata mugunta.


Da Yehoram ya ga Yehu, sai ya ce, “Lafiya dai?” Yehu ya ce, “Ina fa lafiya, tun da karuwanci da sihirin uwarka, Yezebel, sun yi yawa haka?”


Ya ɗauki halin gidan Ahab. Ya aikata mugun abu a gaban Ubangiji kamar yadda gidan Ahab ya yi, gama shi surukin gidan Ahab ne.


Duk da haka, bai rabu da zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi.


Ya aikata zunubi a gaban Ubangiji. Ya bi hanyar Yerobowam da zunubin da ya sa mutanen Isra'ila su yi.


Ahab ya rasu kamar kakanninsa. Ɗansa Ahaziya ya gāji sarautarsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ