“Ka tambayar mana Ubangiji, gama Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kawo mana yaƙi. Ko Ubangiji zai yi mana al'amuran nan nasa masu ban al'ajabi kamar yadda ya saba, ya sa Sarkin Babila ya janye, ya rabu da mu?”
Yehoshafat ya ce, “Ba wani annabin Ubangiji ne a nan, wanda zai tambayar mana Ubangiji?” Sai ɗaya daga cikin fādawan Sarkin Isra'ila ya amsa ya ce, “Ai, akwai Elisha ɗan Shafat, na'ibin Iliya.”
Zai dogara ga Ele'azara, firist, don ya san nufina, ta wurin amfani da Urim da Tummin. Ta haka ne Ele'azara zai bi da Joshuwa da dukan taron jama'ar Isra'ila cikin al'amuransu.”
Sai mala'ikan Ubangiji ya yi magana da Iliya Batishbe, ya ce, “Tashi, ka tafi, ka sadu da manzannin Sarkin Samariya, ka ce musu, ‘Ba Allah a Isra'ila da za ku tafi ku tambayi Ba'alzabul, gunkin Ekron?’
Sai Dawuda ya yi tambaya ga Ubangiji ya ce, “In bi sawun 'yan harin nan? Zan ci musu?” Ya ce masa, “Bi su, gama za ka ci musu, ka ƙwato abin da suka kwashe.”
Sai Dawuda ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ko in tafi in fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi?” Ubangiji kuwa ya ce wa Dawuda, “Tafi, ka yi yaƙi da Filistiyawa, ka ceci mutanen Kaila.”
Isra'ilawa suka tashi suka tafi Betel. A can suka yi tambaya ga Allah suka ce, “Wace kabila ce daga cikinmu za ta fara faɗa wa kabilar Biliyaminu?” Ubangiji ya ce, “Kabilar Yahuza ce za ta fara.”
Ya kuma ce wa Yehoshafat, “Za ka tafi tare da ni zuwa wurin yaƙi a Ramot-gileyad?” Yehoshafat ya amsa wa Sarkin Isra'ila, “Ni da kai ɗaya ne, mutanena kuma mutanenka ne, dawakaina kuma naka ne.”
Sa'an nan Sarkin Isra'ila ya tara annabawa ɗari huɗu, ya tambaye su, ya ce, “In tafi in yi yaƙi da Ramot-gileyad, ko kuwa kada in tafi?” Su kuwa suka ce masa, “Ka haura, gama Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”