Sai Yehu maigani, ɗan Hanani, ya fita domin ya tarye shi, ya ce wa sarki Yehoshafat, “Za ka taimaki mugu ka kuma ƙaunaci maƙiyan Ubangiji? Saboda haka hasalar Ubangiji za ta same ka.
saboda zunubansu da zunuban kakanninsu. Gama suka ƙona turare a ɗakunan tsafin arna na kan tuddai, suka kuwa faɗi mugun abu a kaina. Saboda haka zan hukunta su yadda ya cancance su.”