1 Sarakuna 22:43 - Littafi Mai Tsarki43 Ya bi halin tsohonsa, Asa, bai karkace ba. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji. Duk da haka ba a rushe wuraren tsafin na tuddai ba. Mutane suka yi ta miƙa hadayu, suka ƙona turare a tuddan. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202043 A cikin kome ya yi tafiya a hanyoyin mahaifinsa Asa, bai kuma kauce daga gare su ba; ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji. Amma bai rurrushe masujadai da suke kan tuddai ba, mutane kuwa suka ci gaba da miƙa hadayu suna kuma ƙone turare a can. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Da Asa ya ji irin kalmomin da annabi Azariya ɗan Oded ya hurta, sai ya yi ƙarfin zuciya, ya kawar da gumakan nan masu banƙyama daga dukan ƙasar Yahuza da ta Biliyaminu, daga kuma biranen da ya ci a ƙasar tuddai na Ifraimu. Sa'an nan ya gyara bagaden Ubangiji wanda yake a ƙofar shirayin Haikalin Ubangiji.
Asa kuwa ya yi kuka ga Ubangiji Allahnsa, ya ce, “Ya Ubangiji, ba wani mai taimako kamarka, wanda zai yi taimako sa'ad da mai ƙarfi zai kara da marar ƙarfi, ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama a gare ka muke dogara, da sunanka kuma muka zo don mu yi yaƙi da wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu, kada ka bar mutum ya rinjayi jama'arka.”