Ahaziya kuwa ya mutu bisa ga maganar Ubangiji, daidai yadda Iliya ya faɗa. Sai ɗan'uwansa Yehoram ya gāji gadon sarautarsa a shekara ta biyu ta Yoram ɗan Yehoshafat Sarkin Yahuza, gama Ahaziya ba shi da ɗa.
Ahaziya ya faɗo daga tagar benensa a Samariya, ya kuwa ji ciwo ƙwarai. Sai ya aiki manzanni, ya ce musu, “Ku tafi, ku tambayi Ba'alzabul, gunkin Ekron, ko zan warke daga wannan ciwo.”
Ahaziya, ɗan Ahab, ya ci sarautar Isra'ila a Samariya a shekara ta goma sha bakwai ta sarautar Yehoshafat, Sarkin Yahuza. Ya yi sarautar Isra'ila shekara biyu.
Amma sa'ad da Hadad ya ji labari Dawuda ya rasu, Yowab shugaban sojoji shi ma ya rasu, sai Hadad ya ce wa Fir'auna, “Ka yardar mini, in tashi, in koma ƙasata.”
Ubangiji ya ce wa Musa, “Ga shi, za ka rasu ka tarar da kakanninka. Wannan jama'a kuwa za ta fara kaucewa daga hanya, su bi gumakan ƙasar da za su shiga, su zauna. Za su rabu da ni, su ta da alkawarina wanda na yi da su.
Sauran ayyukan Ahab da dukan abin da ya yi, da gidan da ya gina na hauren giwa da garuruwan da ya gina, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.