Sa'an nan ya sayi tudun Samariya daga Shemer a bakin azurfa dubu shida (6,000), a wurin Shemer, ya kuwa yi gini a kan tudun, ya sa masa suna Samariya saboda sunan Shemer mai tudun.
Sa'an nan annabin ya ce wa sarki, “Ubangiji ya ce, ‘Da yake ka bar mutumin da na ƙaddara ga mutuwa ya kuɓuta daga hannunka, haka ranka zai zama a maimakon nasa, mutanenka kuwa a maimakon mutanensa.’ ”
Na sa masu duba su zama wawaye, Na sassāke annabce-annabcen masanan taurari. Na bayyana kuskuren maganar masu hikima, Na kuma nuna masu hikimarsu wauta ce.
Suna faɗar ƙarya, suna kuma yin duban ƙarya, suna cewa, ‘Ubangiji ya ce,’ alhali kuwa Ubangiji bai aike su ba, duk da haka sun sa zuciya ga cikawar maganarsu.