Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 22:27 - Littafi Mai Tsarki

27 Ku ce musu su jefa wannan mutum a kurkuku, a riƙa ciyar da shi da abinci kaɗan da ruwan sha kaɗan, har na komo lafiya.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 Ku ce ga abin da sarki ya ce, ‘Ku sa wannan mutum a kurkuku, kuma kada ku ba shi wani abu sai dai burodi da ruwa, sai na dawo lafiya.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 22:27
27 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Asa ya yi fushi da maiganin, ya sa shi a kurkuku saboda maganar da ya yi masa, gama ya husata da shi ƙwarai. A wannan lokaci kuma sai Asa ya ƙuntata wa waɗansu daga cikin jama'a.


Kada ka ji tsoron wuyar da za ka sha. Ga shi, Iblis yana shiri ya jefa waɗansunku a kurkuku don a gwada ku, za ku kuwa sha tsanani har kwana goma. Ka riƙi amana ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka kambin rai.


Domin haka, ni Bulus, ɗan sarƙa saboda Almasihu Yesu domin amfanin ku al'ummai,


Na kuwa yi haka a Urushalima, har na sami izini daga manyan firstoci, na kulle tsarkaka da yawa a kurkuku. Har ma a lokacin da ake kashe su ina goyon bayan yin haka.


Sai suka ɗauki Irmiya suka saka shi a rijiyar Malkiya ɗan sarki, wadda take gidan waƙafi. Suka zurara Irmiya a ciki da igiya. Ba ruwa a rijiyar, sai dai lāka, Irmiya ya nutse cikin lākar.


Shugabanni suka yi fushi da Irmiya, suka yi masa dūka, suka tsare shi a gidan Jonatan magatakarda, gama an mai da gidansa ya zama kurkuku.


Ubangiji ya naɗa ka firist a madadin Yehoyada firist, ka lura da Haikalin Ubangiji, ka sa kowane mahaukacin da zai yi annabci a turu, ka sa masa ƙangi.


sai ya sa aka yi wa Irmiya dūka, aka kuma sa shi cikin turu a ƙofar Biliyaminu, a Haikalin Ubangiji.


Ubangiji zai sa ku ku sha wahala, amma shi kansa zai kasance tare da ku, ya koya muku, ba za ku ƙara wahalar nemansa ba.


Ba wani amfani a sha wahalar aiki saboda abinci, A yi asubancin tashi, a yi makarar kwanciya, Gama Ubangiji yakan hutar da waɗanda yake ƙauna.


Toka ce abincina, Hawayena kuwa sun gauraya da abin shana,


Ka ciyar da mu da hawaye, Ka shayar da mu da babban ƙoƙo na hawaye.


Kada ku ci abinci mai yisti tare da hadayar. Kwana bakwai za ku riƙa cin abinci marar yisti tare da hadayar, gama abincin wahala ne, gama da gaggawa kuka fita daga ƙasar Masar, don haka za ku tuna da ranar da kuka fito daga ƙasar Masar dukan kwanakinku.


Har wa yau kuma, waɗansu suka sha ba'a da bulala, har ma da ɗauri da jefawa a cikin kurkuku.


Sarki Ahab ya ce, “Ku kama Mikaiya, ku kai shi wurin Amon, shugaban birnin, da wurin Yowash ɗan sarki.


Da Yehudi ya karanta sakin layi uku ko huɗu sai sarki ya sa wuƙa ya yanke su, ya zuba a wutar da take ci a kasko, da haka ya ƙone littafin duka.


Da sarki ya ji maganar annabin, wato wadda ya yi a kan bagaden da yake Betel, sai ya miƙa hannunsa daga bagaden, ya ce, “Ku kama shi.” Hannun da ya miƙa kuwa ya sage, bai iya komo da shi ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ