Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 22:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Sarki Ahab kuwa ya ce masa, “Sau nawa zan roƙe ka kada ka faɗa mini kome sai dai gaskiya ta Ubangiji?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Sai sarki ya ce masa, “Sau nawa ne zan sa ka rantse cewa ba za ka faɗa mini kome ba sai dai gaskiya a cikin sunan Ubangiji?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 22:16
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai waɗansu Yahudawa masu yawo gari gari, matsubbata, suka yi ƙoƙarin kama sunan Ubangiji Yesu ga masu baƙaƙen aljannu, suna cewa, “Mun umarce ku da sunan Yesun nan da Bulus yake wa'azi.”


ya ƙwala ihu ya ce, “Ina ruwanka da ni, Yesu Ɗan Allah Maɗaukaki? Na gama ka da Allah, kada ka yi mini azaba.”


Amma Yesu na shiru. Sai babban firist ya ce masa, “Na gama ka da Allah Rayayye, ka faɗa mana ko kai ne Almasihu, Ɗan Allah.”


Amma sarki ya ce masa, “Har sau nawa zan rantsar da kai don kada ka faɗa mini kome, sai gaskiya da sunan Ubangiji?”


A ran nan kuwa Isra'ilawa sun sha wahala, gama Saul ya yi rantsuwa mai ƙarfi ya ce, “La'ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin faɗuwar rana tun ban ɗauko fansa a kan abokan gābana ba.” Don haka ba mutumin da ya ɗanɗana abinci.


A lokacin nan Joshuwa ya yi musu magana da rantsuwa ya ce, “La'ananne ne mutum a gaban Ubangiji Wanda ya tashi don ya sāke gina birnin nan Yariko. A bakin ɗan farinsa zai kafa tushensa, A bakin autansa kuma zai gina ƙofofinsa.”


Da ya zo gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Mikaiya, mu tafi Ramot don yaƙi, ko kuwa kada mu tafi?” Ya amsa masa ya ce, “Ka haura, za ka yi nasara, Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”


Mikaiya ya ce, “Na ga mutanen Isra'ila duka a warwatse a kan tuddai kamar tumakin da ba su da makiyayi, Ubangiji kuwa ya ce, ‘Waɗannan ba su da shugaba, bari kowa ya koma gidansa lafiya.’ ”


Sarki Zadakiya ya aika a kawo masa Irmiya. Sarki kuwa ya shigar da shi gidansa, ya tambaye shi a asirce, ya ce, “Ko akwai wata magana daga wurin Ubangiji?” Sai Irmiya ya ce, “Akwai kuwa!” Ya ci gaba ya ce, “Za a ba da kai a hannun Sarkin Babila.”


Sarki Zadakiya ya aika a kirawo annabi Irmiya. Ya tafi ya sadu da Irmiya a ƙofa ta uku ta Haikalin Ubangiji. Sarki kuwa ya ce wa Irmiya, “Zan yi maka tambaya, kada kuwa ka ɓoye mini kome.”


Bal'amu ya amsa wa Balak ya ce, “To, ai, ga shi, na zo yanzu! Ina da wani ikon yin wata magana ne? Maganar da Allah ya sa a bakina, ita zan faɗa, tilas.”


Bari annabin da yake da mafarki ya faɗi mafarkinsa, amma wanda yake da maganata ya faɗe ta da aminci. Me ya haɗa ciyawa da alkama? Ni Ubangiji na faɗa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ