Ben-hadad ya ce masa, “Biranen da tsohona ya ƙwace daga wurin tsohonka, zan mayar maka. Kai kuma za ka yi karauku a Dimashƙu kamar yadda tsohonka ya yi a Samariya.” Sai Ahab ya ce, “Zan bar ka, ka tafi a kan wannan sharaɗi.” Ya kuwa yi alkawari da shi, sa'an nan ya bar shi, ya tafi.
“Ka ga yadda Ahab ya ƙasƙantar da kansa a gabana? Da yake ya ƙasƙantar da kansa a gabana, ba zan kawo masifar a zamaninsa ba, sai a zamanin ɗansa ne, zan kawo masifar a kan gidansa.”