“Ka ga yadda Ahab ya ƙasƙantar da kansa a gabana? Da yake ya ƙasƙantar da kansa a gabana, ba zan kawo masifar a zamaninsa ba, sai a zamanin ɗansa ne, zan kawo masifar a kan gidansa.”
Da Ubangiji ya ga sun ƙasƙantar da kansu, sai ya yi magana da Shemaiya cewa, “Tun da yake sun ƙasƙantar da kansu, to, ba zan hallaka su ba, amma zan cece su, ba zan kwararo fushina ta hannun Shishak a kan Urushalima ba.