Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 21:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Sai Ahab ya yi magana da Nabot ya ce, “Ka ba ni gonar inabinka don in mai da ita lambu, gama gonar tana kusa da gidana, ni kuwa zan ba ka wata gonar inabi a maimakonta, idan kuma kana so, sai in ba ka tamanin kuɗinta.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Sai Ahab ya ce wa Nabot, “Ka ba ni gonar inabinka in yi amfani da ita don kayan lambu, da yake tana kusa da fadana. Zan ba ka wata gonar inabin da ta fi wannan, ko kuma in ka gwammace, sai in biya ka duk abin da ya dace da ita.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 21:2
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Zai ƙwace gonakinku mafi kyau, da gonakinku na inabi, da gonakinku na zaitun, ya ba fādawansa.


Masu ɗokin yin arziki kuwa, sukan zarme da jaraba, su fāɗa a cikin tarko, suna mugayen sha'awace-sha'awace iri iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka.


Ya kuma ce musu, “Ku kula fa, ku yi nesa da kowane irin kwaɗayi, don yawan kaya ba shi ne rai ba.”


Amma ka sa idonka da zuciyarka ga ƙazamar riba, Da zubar da jinin marar laifi, Da yin zalunci da danniya.


Maɓuɓɓugai suna ba lambun ruwa, ruwan rafuffuka suna gudu, Ƙoramu suna bulbulo ruwa daga Dutsen Lebanon.


Na kuma yi wa kaina lambuna da gonakin itatuwa, ba irin itatuwa masu 'ya'ya da ba su a ciki.


Da Ahaziya Sarkin Yahuza, ya ga haka, sai ya gudu ta hanyar Bet-haggan.Yehu kuwa ya bi shi, ya ce, “Shi ma a harbe shi.” Sai suka harbe shi a cikin karusarsa a hawan Gur, wanda yake kusa da Ibleyam. Sai ya gudu zuwa Magiddo, ya mutu a can.


Akish kuwa ya kira Dawuda, ya ce masa, “Kai amintacce ne a ganina, daidai ne kuma ka tafi yaƙi tare da ni, gama ban same ka da wani laifi ba tun daga ranar zuwanka wurina har yau, duk da haka sarakunan ba su amince da kai ba.


Amma Sama'ila bai ji daɗin roƙonsu ba, na a naɗa musu sarki, saboda haka ya yi addu'a ga Ubangiji.


Gama ƙasar da za ku shiga garin ku mallake ta, ba kamar ƙasar Masar take ba inda kuka fito, inda kukan shuka iri sa'an nan ku yi ta zuwa kuna banruwa kamar lambu.


“ ‘Kada ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka. Kada kuma ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka, ko gonarsa, ko barorinsa mata ko maza, ko sansa, ko jakinsa, ko kowane abu da yake na maƙwabcinka.’


“Kada ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka. Kada kuma ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka, ko barorinsa mata da maza, ko sansa, ko jakinsa, ko kowane abin da yake nasa.”


Amma Abram ya ce wa Saraya, “Ga shi, baranyarki tana cikin ikonki, yi yadda kika ga dama da ita.” Saraya ta ƙanƙanta ta, sai Hajaratu ta gudu daga gare ta.


Matar ta ga yadda itacen yana da kyau, 'ya'yansa kuma kyawawa, abin sha'awa ne kuma ga ido, abin marmari ne domin ba da hikima, ta tsinka daga 'ya'yansa, ta kuwa ci, ta kuma bai wa mijinta waɗansu, shi kuma ya ci.


Amma Nabot ya ce wa Ahab, “Ubangiji ya sawwaƙa in ba ka gādon kakannina.”


Ya ce mata, “Domin na yi magana da Nabot Bayezreyele, na ce ya sayar mini da gonar inabinsa, idan kuma yana so, sai in ba shi wata gonar inabi a maimakon tasa, amma ya ce ba zai ba ni gonar inabin ba.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ