Ubangiji yana zuwa ya hukunta jama'arsa a duniya saboda zunubansu. Kashe-kashen da aka yi a duniya a ɓoye, za a bayyana su, ƙasa ba za ta ƙara ɓoye waɗanda aka kashe ba.
Amma Elisha ya ce masa, “Ashe, ba ina tare da kai a ruhu ba, sa'ad da mutumin ya juyo daga karusarsa don ya tarye ka? Wannan shi ne lokacin karɓar kuɗi, da riguna, da gonaki na zaitun, da na inabi, da tumaki, da shanu, da barori mata da maza?
Sai mala'ikan Ubangiji ya yi magana da Iliya Batishbe, ya ce, “Tashi, ka tafi, ka sadu da manzannin Sarkin Samariya, ka ce musu, ‘Ba Allah a Isra'ila da za ku tafi ku tambayi Ba'alzabul, gunkin Ekron?’