Dubi aikin banza da yake faruwa a duniya. Wani lokaci adalai suke shan hukuncin da za a yi wa mugaye, mugaye kuwa su karɓi sakayyar da za a ba adalai. Na ce wannan ma aikin banza ne.
Idan ka ga hukuma na zaluntar talakawa, ba ta yi musu adalci, ba ta kiyaye hakkinsu, kada ka yi mamaki. Kowane shugaba yana da shugaban da yake goyon bayansa. Dukansu biyu suna da goyon bayan manyan shugabanni.
Nan da nan da Yezebel ta ji an jajjefi Nabot har ya mutu, sai ta ce wa Ahab, “Tashi, ka mallaki gonar inabin Nabot, wadda ya ƙi sayar maka, gama Nabot ba shi da rai, ya mutu.”