1 Sarakuna 20:25 - Littafi Mai Tsarki25 Sa'an nan ka tara sojoji kamar yawan waɗanda ka rasa, ka kuma tara dawakai a maimakon na dā, da karusai a maimakon karusai na dā. Mu kuwa za mu yi yaƙi da su a kwari. Ba shakka za mu ci su.” Sarki Ben-hadad ya ji maganarsu, ya kuwa yi haka nan. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202025 Dole kuma ka tā da waɗansu mayaƙa kamar waɗanda ka rasa, doki don doki, keken yaƙi kuma don keken yaƙi, saboda mu iya yaƙe Isra’ila a fili. Ta haka tabbatacce za mu fi ƙarfinsu.” Sai ya yarda da su, ya kuma yi haka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |