Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 2:29 - Littafi Mai Tsarki

29 Sa'ad da aka faɗa wa sarki Sulemanu, Yowab ya gudu zuwa alfarwa ta Ubangiji, ga shi, yana wajen bagade, sai Sulemanu ya aiki Benaiya, ɗan Yehoyada, ya je ya kashe shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

29 Aka faɗa wa Sarki Solomon cewa Yowab ya gudu zuwa tentin Ubangiji, yana kuma kusa da bagade. Sai Solomon ya umarci Benahiya ɗan Yehohiyada ya ce, “Je ka kashe shi!”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 2:29
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Sarki Sulemanu ya aiki Benaiya ɗan Yehoyada, ya kashe Adonija.


Amma idan mutum ya fāɗa wa ɗan'uwansa da niyyar kisankai, lalle, sai a kashe shi ko da ya gudu zuwa bagadena.


Don lokaci ya yi da za a fara shari'a ta kan jama'ar Allah. In kuwa ta kanmu za a fara, to, me zai zama ƙarshen waɗanda ba su bi bisharar Allah ba?


Ku kashe tsofaffi, da samari, da 'yan mata, da ƙananan yara, da mata, amma kada ku taɓa wanda yake da shaida. Sai ku fara a Haikalina.” Suka kuwa fara da dattawan da suke a gaban Haikalin.


Sa'an nan sarki ya umarci Benaiya ɗan Yehoyada, ya tafi, ya kashe Shimai. Yanzu sarauta ta tabbata a hannun Sulemanu.


Sarki kuwa ya ce masa, “Ka yi yadda ya ce, ka kashe shi, ka binne shi, ta haka za ka kawar mana da hakkin jinin da Yowab ya zubar ba dalili.


Benaiya ɗan Yehoyada, shi ne shugaban Keretiyawa da Feletiyawa, wato matsara. 'Yan'yan Dawuda, maza, suka zama mataimakansa.


Benaiya kuwa ya tafi alfarwa ta Ubangiji, ya ce masa, “Sarki ya ce ka fito.” Amma Yowab ya ce, “A'a, a nan zan mutu.” Benaiya kuma ya je ya faɗa wa sarki abin da Yowab ya ce.


Mutumin da yake da laifin kisankai, yana haƙa wa kansa kabari da gaggawa. Kada ka yi ƙoƙarin hana shi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ