Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 2:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Sa'an nan Bat-sheba ta tafi wurin sarki Sulemanu don ta yi magana da shi a kan Adonija. Sarki ya tashi domin ya tarye ta. Ya rusuna mata, sa'an nan ya zauna a kujerar sarautarsa. Ya sa aka kawo mata kujera, ta kuwa zauna a wajen damansa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Sai Batsheba ta tafi wurin Sarki Solomon don tă yi masa magana a kan Adoniya. Sarki ya miƙe tsaye don yă sadu da ita, ya rusuna mata, ya kuma zauna a kujerar sarautarsa. Ya sa aka kawo wa mahaifiyar sarki kujerar sarauta, ta kuwa zauna a gefen damansa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 2:19
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Daga cikin matan da suke fadarka, har da 'ya'yan sarakuna. A daman kursiyinka kuwa ga sarauniya a tsaye. Tana saye da kayan ado na zinariya mafi kyau duka.


Ubangiji ya ce wa Mai Girma, Sarkina, “Zauna nan a damana, Har in sa maƙiyanka a ƙarƙashin sawayenka.”


Ya kuma fitar da tsohuwarsa Ma'aka daga zaman sarauniya, domin ta yi ƙazantacciyar siffa ta gunkiyar Ashtoret. Asa ya sassare siffar, ya ƙone ta a rafin Kidron.


“Ku girmama tsofaffi ku darajanta su, gama kuna tsorona. Ni ne Ubangiji.


Sai ko wannenku ya girmama mahaifiyarsa da mahaifinsa, ya kuma kiyaye lokatan sujada. Ni ne Ubangiji Allahnku.


“Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.


Zai sa tumaki a damansa, awaki kuwa a hagunsa.


Bat-sheba kuwa ta ce, “Da kyau, zan yi wa sarki magana dominka.”


Yusufu ya kawar da su daga gwiwoyin Isra'ila, ya sunkuyar da fuskarsa har ƙasa a gabansa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ