Ta ce masa, “To, sai ka faɗa.” Sai ya ce, “In kin yarda ki yi magana da sarki Sulemanu, gama ba zai ƙi jinki ba, ki ce ya ba ni yarinyar nan, Abishag, daga Shunem, ta zama matata.”
Sa'an nan Bat-sheba ta tafi wurin sarki Sulemanu don ta yi magana da shi a kan Adonija. Sarki ya tashi domin ya tarye ta. Ya rusuna mata, sa'an nan ya zauna a kujerar sarautarsa. Ya sa aka kawo mata kujera, ta kuwa zauna a wajen damansa.