Ya amsa ya ce, “Kin sani dai sarauta tawa ce. Ni ne kuwa mutanen Isra'ila duka suka sa zuciya zan ci sarautar, amma al'amarin ya sāke, sai sarautar ta zama ta ƙanena, gama tasa ce bisa ga nufin Allah.
Ta ce masa, “To, sai ka faɗa.” Sai ya ce, “In kin yarda ki yi magana da sarki Sulemanu, gama ba zai ƙi jinki ba, ki ce ya ba ni yarinyar nan, Abishag, daga Shunem, ta zama matata.”
Sai ta ce, “Ina da wani ɗan roƙo a gare ka, kada ka hana mini shi.” Sarki ya ce mata, “Ya tsohuwata, sai ki faɗi abin da kike so, gama ba zan hana miki ba.”