Sulemanu ya gama kai da Fir'auna, Sarkin Masar, ta wurin aure, domin ya auri 'yar Fir'auna, ya kawo ta birnin Dawuda kafin ya gama ginin gidan kansa, da Haikalin Ubangiji, da garun Urushalima.
Amma sa'ad da Hadad ya ji labari Dawuda ya rasu, Yowab shugaban sojoji shi ma ya rasu, sai Hadad ya ce wa Fir'auna, “Ka yardar mini, in tashi, in koma ƙasata.”
Sai Sulemanu ya sa dattawan Isra'ila duka, da shugabannin kabilai, da shugabannin dangi dangi na Isra'ila, su hallara a gabansa a Urushalima, domin su kawo akwatin alkawari na Ubangiji daga Sihiyona, birnin Dawuda, zuwa Haikali.
Ahaziya, ɗan Ahab, ya ci sarautar Isra'ila a Samariya a shekara ta goma sha bakwai ta sarautar Yehoshafat, Sarkin Yahuza. Ya yi sarautar Isra'ila shekara biyu.