Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 19:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Sai Iliya ya tashi ya ci abinci ya sha ruwa ya sami ƙarfi, sa'an nan ya kama tafiya kwana arba'in dare da rana har zuwa Horeb, wato dutsen Allah.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Saboda haka ya tashi ya ci, ya kuma sha. Ta wurin ƙarfin da ya samu saboda wannan abinci, ya yi tafiya yini arba’in da dare arba’in, sai da ya kai Horeb, dutsen Allah.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 19:8
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Musa kuwa yana tare da Ubangiji yini arba'in da dare arba'in, bai ci ba, bai sha ba. Sai ya rubuta kalmomin alkawarin a kan allunan, wato dokokin nan goma.


Da ya yi azumi kwana arba'in ba dare ba rana, daga baya yunwa ta kama shi.


Sai na fāɗi ƙasa, na kwanta a gaban Ubangiji dare arba'in da yini arba'in, ban ci ba, ban sha ba, kamar yadda na yi a dā, saboda dukan zunubin da kuka aikata, kuka yi abin da yake mugu ga Ubangiji, kuka tsokane shi.


Sai Musa ya shiga girgijen, ya hau bisa dutsen. Ya zauna a kan dutsen yini arba'in da dare arba'in.


Wata rana, sa'ad da Musa yake kiwon garken surukinsa, Yetro, firist na Madayana, sai ya kai garken yammacin jeji, har ya zo Horeb, wato dutsen Allah.


amma ya ce mini, “Alherina yā isa, domin ta wajen rashin ƙarfi ake ganin cikar ikona.” Saboda haka sai ma in ƙara yin alfarma da raunanata da farinciki fiye da na da, domin ikon Almasihu ya zauna a tare da ni.


har kwana arba'in, Iblis yana gwada shi. A kwanakin nan bai ci kome ba. Da suka ƙare kuwa ya ji yunwa.


Yana jeji har kwana arba'in, Shaiɗan na gwada shi, yana tare da namomin jeji, mala'iku kuma suna yi masa hidima.


A ƙarshen kwana goma ɗin, sai aka ga fuskokinsu suna sheƙi, sun kuma yi ƙiba fiye da samarin da suke cin abinci irin na sarki.


Ga shi, hayaƙi ya tunnuƙe dutsen Sina'i duka, saboda Ubangiji ya sauko a bisa dutsen da wuta. Hayaƙi kuwa ya tunnuƙe, ya yi sama kamar na wurin narka ma'adinai, dutsen duka ya girgiza ƙwarai.


Sai Ubangiji ya ce wa Haruna, “Tafi, ka taryi Musa cikin jeji.” Ya kuwa tafi ya tarar da shi a dutsen Allah, ya sumbace shi.


Mala'ikan Ubangiji kuma ya sake zuwa sau na biyu, ya taɓa shi, ya ce, “Tashi, ka ci abinci, in ba haka ba kuwa tafiya za ta gagare ka.”


Hankaki kuma suka riƙa kawo masa abinci da nama, safe da maraice. Yakan kuma sha ruwa daga rafin.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ