1 Sarakuna 19:21 - Littafi Mai Tsarki21 Elisha kuwa ya koma, ya kama shanun noman, ya yanka, ya dafa su da karkiyoyinsu. Ya raba wa mutane, suka ci. Sa'an nan ya tashi, ya bi Iliya, ya zama mai taimakonsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202021 Sai Elisha ya bar shi, ya koma, ya ɗauki shanunsa ya yayyanka. Ya ƙone kayan garman noman don yă dafa naman, ya kuma ba wa mutane naman, suka kuwa ci. Sa’an nan ya tashi, ya bi Iliya, ya kuma zama mai hidimarsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |