Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 19:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Bayan girgizar kuma, sai wuta, amma Ubangiji ba ya cikin wutar. Bayan wutar sai ƙaramar murya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Bayan girgizar ƙasa, sai ga wuta, amma Ubangiji ba ya cikin wuta. Bayan wutar kuma sai ga wata ’yar murya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 19:12
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Na ga wani abu can yana tsaye, Na zura ido, amma ban san kowane irin abu ba ne, Ina cikin wannan hali sai na ji murya,


Sa'an nan ya ce, “Wannan ita ce maganar Ubangiji zuwa ga Zarubabel cewa, ‘Ba da ƙarfi, ko iko ba, amma da Ruhuna,’ in ji Ubangiji Mai Runduna.


Akwai wata jama'a da ta taɓa jin muryar wani allah tana magana ta tsakiyar wuta kamar yadda kuka ji, har suka rayu?


Don haka kada ka razana saboda ni, Abin da zan faɗa maka, ba abin da zai fi ƙarfinka.


Ya kuma gifta a gaban Musa, ya ce, “Ni ne Ubangiji, Ubangiji Allah mai jinƙai, mai alheri, mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna, mai gaskiya.


A can mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare shi cikin harshen wuta daga cikin kurmi. Da Musa ya duba, sai ga kurmin yana cin wuta, amma duk da haka bai ƙone ba.


Sa'ad da rana ta fāɗi aka kuwa yi duhu, sai ga tanderun wuta mai hayaƙi da jiniya mai harshen wuta suka ratsa tsakanin abubuwan nan da aka tsattsaga a tsaka.


farat ɗaya, sai aka ji wani amo daga sama, kamar na busowar gawurtacciyar iska, ya cika duk gidan da suke zaune.


Da suka ci gaba da tafiya suna taɗi, sai ga karusar wuta da dawakan wuta suka raba su. Aka ɗauke Iliya zuwa Sama cikin guguwa.


Iliya ya ce wa shugaban da mutum hamsin ɗin, “Idan ni mutumin Allah ne, bari wuta ta sauko daga sama ta cinye ka da mutane naka hamsin.” Wuta kuwa ta sauko daga sama, ta cinye shugaban tare da mutanensa hamsin.


Ubangiji kuwa ya sa wuta ta faɗo, ta cinye hadaya ta ƙonawa, da itacen, da duwatsun, da ƙurar, ta kuma lashe ruwan da yake cikin wuriyar.


“Domin haka, sai ku kula da kanku sosai, gama ba ku ga siffar kome ba sa'ad da Ubangiji Allahnku ya yi magana da ku a Horeb ta tsakiyar wuta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ