Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 19:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Ubangiji ya ce masa, “Tafi, ka tsaya a kan dutse, a gabana.” Sai ga Ubangiji yana wucewa, babbar iska mai ƙarfi ta tsage dutsen, amma Ubangiji ba ya cikin iskar. Bayan iskar sai girgizar ƙasa, amma Ubangiji ba ya cikin girgizar ƙasar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Sai Ubangiji ya ce, “Fita ka tsaya a kan dutse a gaban Ubangiji, gama Ubangiji yana shirin wucewa.” Sai ga babbar iska mai ƙarfi ta tsage duwatsu, ta kuma ragargaza duwatsu a gaban Ubangiji, amma Ubangiji ba ya cikin iskar. Bayan iskar sai aka yi girgizar ƙasa, amma Ubangiji ba ya cikin girgizar ƙasa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 19:11
31 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da na duba, sai ga hadiri mai iska ya taso daga wajen arewa, da wani babban girgije da haske kewaye da shi, da wuta tana ta ci falfal. A tsakiyar wutar wani abu yana walƙiya kamar tagulla.


Allahnmu ya zo, ba a ɓoye yake ba, Wuta mai cinyewa na tafe a gabansa, Babban hadiri kuwa na kewaye da shi.


Ubangiji zai bar kowane mutum ya ji maɗaukakiyar muryarsa, ya kuma ji ƙarfin fushinsa. Za a ga harsunan wuta, gizagizai za su ɓarke, za a yi ƙanƙara, da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.


Ubangiji ya yi magana da Ayuba ta cikin guguwa.


A lokacin nan muryarsa ta girgiza duniya, amma a yanzu ya yi alkawari cewa, “Har wa yau dai sau ɗaya tak, ba duniya kaɗai zan girgiza ba, amma har sama ma.”


Sai na yi annabci kamar yadda ya umarce ni. Da na yi annabcin sai aka ji motsi da girgiza. Sai ƙasusuwan suka harhaɗu da juna, ƙashi ya haɗu da ƙashi a mahaɗinsu.


Duniya ta girgiza, sararin sama ya kwararo ruwa, Saboda bayyanar Allah, har Dutsen Sinai ya girgiza, Saboda bayyanar Allah na Isra'ila.


Da safe ka shirya, ka zo Dutsen Sina'i ka gabatar da kanka gare ni a kan dutsen.


Ubangiji ya sauko bisa dutsen Sina'i bisa ƙwanƙolin dutsen. Ya kirawo Musa zuwa ƙwanƙolin dutsen, Musa kuwa ya hau.


Sa'an nan na ga wani babban kursiyi fari, da wanda yake a zaune a kai, sai sama da ƙasa suka guje wa Zatinsa, suka ɓace.


Sai aka yi ta walƙiya, da ƙararraki masu tsanani, da aradu, da wata babbar rawar ƙasa irin wadda ba a taɓa yi ba, tun da ɗan adam yake a duniya, gawurtacciyar rawar ƙasa ƙwarai da gaske.


Sa'an nan aka buɗe Haikalin nan na Allah da yake a Sama, aka kuma ga akwatin alkawarinsa a Haikalinsa. Sai aka yi ta walƙiya da kururuwa, da aradu, da rawar ƙasa, da ƙanƙara manya manya.


Sai Musa ya shiga girgijen, ya hau bisa dutsen. Ya zauna a kan dutsen yini arba'in da dare arba'in.


Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka hawo zuwa wurina a bisa dutsen, ka zauna har in ba ka allunan dutse da yake da dokoki da farillan da na rubuta don a koya musu.”


Sai kuwa aka yi wata babbar rawar ƙasa, domin wani mala'ikan Ubangiji ne ya sauko daga Sama, ya zo ya mirgine dutsen, ya zauna a kai.


Sa'an nan ya ce, “Wannan ita ce maganar Ubangiji zuwa ga Zarubabel cewa, ‘Ba da ƙarfi, ko iko ba, amma da Ruhuna,’ in ji Ubangiji Mai Runduna.


Ubangiji mai jinkirin fushi ne, Mai Iko Dukka. Ubangiji ba zai kuɓutar da mai laifi ba. Hanyarsa tana cikin guguwa da cikin hadiri, Gizagizai su ne ƙurar ƙafafunsa.


Ya kuma gifta a gaban Musa, ya ce, “Ni ne Ubangiji, Ubangiji Allah mai jinƙai, mai alheri, mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna, mai gaskiya.


Da jama'a suka ji tsawar hadiri, da ƙarar ƙaho mai tsanani suka kuma ga walƙiya, da dutsen yana hayaƙi, sai suka ji tsoro suka yi rawar jiki, suka tsaya nesa.


Al'umma za ta tasar wa al'umma, mulki ya tasar wa mulki. Za a kuma yi yunwa da raurawar ƙasa a wurare dabam dabam.


Za ku gudu zuwa kwarin duwatsuna, gama kwarin duwatsu zai kai har Azel, kamar yadda kakanninku suka gudu a zamanin Azariya, Sarkin Yahuza, a lokacin da aka yi girgizar ƙasa. Sa'an nan Ubangiji Allahna zai zo tare da dukan tsarkakansa!


Dukan Filistiyawan da suke a filin suka ji tsoro, da mahara da sauran sojoji suka yi rawar jiki, ƙasa ta girgiza, aka yi babbar gigicewa.


A safiyar rana ta uku aka yi tsawa, da walƙiyoyi, da girgije mai duhu a bisa dutsen, aka tsananta busar ƙaho, sai dukan jama'ar da suke cikin zango suka yi rawar jiki.


Ka sa aka yi ruwan sama mai yawa, ya Allah, Ka rayar da ƙasarka wadda ta zozaye.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ