Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 18:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Sa'ad da Obadiya yake tafiya a hanya suka yi kaciɓis da Iliya, Obadiya kuwa ya rabe da shi, sai ya rusuna ya ce, “Shugabana Iliya, kai ne kuwa?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Yayinda Obadiya yana tafiya, sai Iliya ya sadu da shi. Obadiya ya gane shi, ya rusuna har ƙasa, ya ce, “Kai ne, shugabana, Iliya?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 18:7
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

To, kallon me kuka fita? Wani mai adon alharini? Ai kuwa, masu adon alharini a fada suke.


Yahaya kuwa yana saye da tufa ta gashin raƙumi, yana kuma ɗaure da ɗamara ta fata, abincinsa kuwa fara ce da ruwan zuma.


'Ya'ya maza na waɗanda suka zalunce ki za su zo, Su rusuna, su nuna bangirma. Dukan waɗanda suka raina ki za su yi sujada a ƙafafunki. Za su ce da ke, ‘Birnin Ubangiji,’ ‘Sihiyona, Birni na Allah Mai Tsarki na Isra'ila.’


A sa'ad da Yerobowam ya fita Urushalima, sai annabi Ahija mutumin Shilo ya tarar da shi a hanya. Lokacin kuwa Ahija yana saye da sabuwar riga, ba kowa a filin sai su biyu kaɗai,


Suka haye zuwa wancan hayi don su hawo da iyalin sarki, su kuma yi masa abin da zai ji daɗi. Sa'ad da sarki yake shirin hayewa, sai Shimai ɗan Gera ya zo ya fāɗi a gābansa.


Da yaron ya tafi, sai Dawuda ya tashi daga inda ya ɓuya kusa da tarin duwatsun, ya rusuna har sau uku. Sa'an nan suka sumbaci juna, suka yi kuka, amma Dawuda ya fi yi.


Sai ya ce wa Musa, “Ya shugabana, ina roƙonka, kada ka hukunta mu saboda wannan zunubi, mun yi aikin wauta.


'Yan'uwansa kuma suka zo suka fāɗi a gabansa, suka ce, “Ga shi, mu barorinka ne.”


Domin haka fa, ina roƙonka, bari ni baranka in zama bawa gare ka, shugabana, a maimakon saurayin a bar saurayin ya koma tare da 'yan'uwansa.


Sai muka amsa, ranka ya daɗe, muka ce, ‘Muna da mahaifi, tsoho, da ɗan tsufansa, auta, wanda ɗan'uwansa ya rasu, shi kaɗai ya ragu daga cikin mahaifiyarsa, mahaifinsa kuwa yana ƙaunarsa.’


Sai Yahuza ya amsa, “Me za mu ce wa shugabana? Wace magana za mu yi? Ko kuwa, ta yaya za mu baratar da kanmu? Allah ne ya tona laifin bayinka, ga mu, mu bayin shugabana ne, da mu da shi wanda aka sami finjalin a wurinsa.”


Sai Saratu ta yi dariya a ranta, tana cewa, “Bayan na tsufa mai gidana kuma ya tsufa sa'an nan zan sami wannan gatanci?”


Da ya ɗaga idonsa, ya duba sai ga mutum uku suna tsaye a gabansa. Da ya gan su, sai ya sheƙa da gudu daga ƙofar alfarwar, don ya tarye su. Ya yi ruku'u,


Saboda haka suka rabu biyu don su zagaya. Ahab ya bi waje guda, shi kuma ya bi ɗaya wajen.


Iliya ya amsa masa ya ce, “Ni ne. Tafi, ka faɗa wa shugabanka, sarki, cewa ga ni nan.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ