Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 18:43 - Littafi Mai Tsarki

43 Sa'an nan ya ce wa baransa, “Ka tafi ka duba wajen teku.” Baran kuwa ya tafi ya duba, ya komo ya ce, “Ban ga kome ba.” Sai ya ce, “Ka yi tafiya kana dubawa, har sau bakwai.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

43 Ya ce wa bawansa, “Tafi ka dubi wajen teku.” Sai bawan ya haura ya duba. Ya ce, “Ba kome a can.” Sau bakwai Iliya ya ce, “Koma.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 18:43
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Gama har yanzu wahayin yana jiran lokacinsa, Yana gaggautawa zuwa cikarsa, Ba zai zama ƙarya ba. Ka jira shi, ko da ka ga kamar yana jinkiri, Hakika zai zo, ba zai makara ba.


a koyaushe kuna addu'a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fāsawa. A kan wannan manufa ku tsaya da kaifinku da matuƙar naci, kuna yi wa dukan tsarkaka addu'a.


Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke yi masa kuka dare da rana hakkinsu ba? Zai yi jinkiri a wajen taimakonsu ne?


Ya kuma ba su wani misali cewa ya kamata kullum su yi addu'a, kada kuma su karai.


A gare ka zan yi addu'a, ya Ubangiji, Da safe za ka ji muryata, Da hantsi zan yi addu'ata, In kuma jira amsa.


Sa'an nan sai mutumin ya ce, “Ka bar ni in tafi, gama gari na wayewa.” Amma Yakubu ya ce, “Ba zan bar ka ka tafi ba, sai ka sa mini albarka.”


Sai Ahab ya haura don ya ci ya sha, Iliya kuwa ya hau can ƙwanƙolin Karmel, ya zauna ƙasa, ya haɗa kai da gwiwa.


A zuwa na bakwai sai ya ce, “Na ga wani ɗan girgije kamar tafin hannu yana tasowa daga teku.” Iliya kuma ya ce, “Tafi, ka faɗa wa Ahab ya shirya karusarsa ya sauka don kada ruwan sama ya hana shi sauka.”


Sai firistoci bakwai su riƙe ƙahonin raguna a gaban akwatin alkawari. Amma a rana ta bakwai za ku zaga birnin sau bakwai, firistoci su yi ta busar ƙahoni.


Elisha ya tashi, ya yi ta kai da komowa a cikin gidan, sa'an nan ya sāke hawan ɗakin, ya miƙe a kan yaron, sai yaron ya yi atishawa har sau bakwai, yaron kuma ya buɗe idanu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ