1 Sarakuna 18:4 - Littafi Mai Tsarki4 A lokacin da Yezebel ta karkashe annabawan Ubangiji, Obadiya ya kwashe annabawa ɗari ya raba su hamsin hamsin ya ɓoye su a kogo, ya ciyar da su, ya shayar da su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20204 Yayinda Yezebel tana kisan annabawan Ubangiji, Obadiya ya ɗauki annabawa ɗari ya ɓoye a kogwanni biyu, hamsin a kowanne, ya kuma tanada musu abinci da kuma ruwa.) အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Elisha kuwa yana zaune a gidansa, dattawa kuma suna zaune tare da shi. Sai sarki ya aiki mutum, amma kafin mutumin ya isa, sai Elisha ya ce wa dattawan, “Kun ga yadda mai kisankan nan ya aiko don a fille mini kai? Idan mutumin ya zo, sai ku rufe ƙofar, ku riƙe ta da ƙarfi. Ba da jimawa ba sarki zai bi bayansa.”