Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 18:39 - Littafi Mai Tsarki

39 Sa'ad da dukan mutane suka ga haka, sai suka rusuna suka sunkuyar da kai suka ce, “Ubangiji shi ne Allah, Ubangiji shi ne Allah.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

39 Sa’ad da mutane suka ga wannan, sai suka rusuna, suka sunkuyar da kai suka ce, “Ubangiji, shi ne Allah! Ubangiji, shi ne Allah!”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 18:39
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Za ku yi kira ga sunan Ba'al naku, ni kuma zan kira ga sunan Ubangiji. Allahn da ya amsa da wuta, shi ne Allah.” Jama'a duka suka yi sowar nuna yarda da wannan.


Sa'ad da dukan Isra'ilawa suka ga wuta ta sauko daga sama, ɗaukakar Ubangiji kuma na cike da Haikalin, sai suka sunkuyar da kansu ƙasa, suka yi sujada, suka yabi Ubangiji, saboda nagarinsa da madawwamiyar ƙaunarsa.


Iliya kuwa ya zo kusa da jama'a ya ce, “Har yaushe za ku daina yawo da hankalinku? Idan Ubangiji shi ne Allah, to, ku bauta masa, in kuwa Ba'al ne Allah, to, ku bauta masa.” Mutane duk suka yi tsit, ba su ce uffan ba.


suka ce, “Yaya za mu yi da mutanen nan? Don hakika sanannen abu ne ga dukan mazauna Urushalima, cewa an yi wata tabbatacciyar mu'ujiza ta wurinsu, ba mu kuwa da halin yin mūsawa.


To, da suka ji haka, maganar ta soke su a zuci, suka ce wa Bitrus da sauran manzannin, “'Yan'uwa, me za mu yi?”


Yahaya fitila ne mai ci, mai haske kuma, kun kuwa yarda ku yi farin ciki matuƙa da haskensa ɗan lokaci kaɗan.


Dawuda ya ɗaga idonsa, sai ya ga mala'ikan Ubangiji yana tsakanin sama da ƙasa, da takobinsa a zare a hannunsa a kan Urushalima. Sa'an nan Dawuda tare da dattawa suka fāɗi rubda ciki, suna saye da tufafin makoki.


Sa'ad da harshen wutar ya hau zuwa samaniya daga bagaden, sai mala'ikan Ubangiji ya hau zuwa sama ta cikin harshen wutar bagaden. Manowa da matarsa sun gani, suka fāɗi a fuskokinsu a ƙasa.


Wuta kuma ta fito daga wurin Ubangiji, ta ƙone hadaya ta ƙonawa da kitsen a bisa bagaden. Da jama'a duka suka gani, suka yi ihu, suka fāɗi rubda ciki suka yi sujada.


domin dukan al'umman duniya su sani Ubangiji shi kaɗai ne Allah, banda shi, ba wani.


Duk wanda yake na mutanensa da yake nan Ubangiji Allahnsa ya kasance tare da shi, bari ya haura zuwa can Urushalima ta ƙasar Yahuza don ya sāke gina Haikalin Ubangiji, Allah na Isra'ila, shi ne Allah wanda ake masa sujada a Urushalima.


Kada fa a manta da cewa, Ubangiji shi ne Allah! Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne, Mu jama'arsa ne, mu garkensa ne.


Ubangiji shi ne Allah, yana yi mana alheri, Ku ɗauki hadayunku ku yi ta idi, Ku ɗaura su a zankayen bagade.


“Ni ne Ubangiji Allahnka wanda ya fisshe ka daga ƙasar Masar, daga gidan bauta.


Ba da jimawa ba, sai ga annabi ya zo wurin sarki Ahab na Isra'ila, ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Ka ga wannan babban taron sojoji? Zan ba da su a hannunka yau, za ka kuwa sani ni ne Ubangiji.’ ”


Sa'ad da ya yi addu'a gare shi, Allah ya karɓi roƙonsa da hurwarsa, ya sāke komar da shi Urushalima da mulkinsa. Sa'an nan ne Manassa ya sani Ubangiji shi ne Allah.


“Ku ji, ya ku jama'ata, zan kuwa yi magana, Zan ba da shaida gāba da ku, ya Isra'ila. Ni ne Allah, Allahnku.


Wa zai tsaya mini gāba da mugaye? Wa zai goyi bayana gāba da masu aikata mugunta?


Ka ce musu, ni Ubangiji Allah, na ce a ranar da na zaɓi Isra'ila na ta da hannuna, na rantse wa zuriyar Yakubu, na kuma bayyana kaina a gare su a ƙasar Masar, cewa ni ne Ubangiji Allahnsu,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ