1 Sarakuna 18:37 - Littafi Mai Tsarki37 Ka amsa mini, ya Ubangiji, ka amsa mini, domin waɗannan mutane su sani, kai Ubangiji, kai ne Allah, kai ne kuma ka juyo da zuciyarsu.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202037 Ka amsa mini, ya Ubangiji, ka amsa mini, saboda waɗannan mutane su san cewa kai, ya Ubangiji, kai ne Allah, su kuma san cewa kana sāke juye zukatansu zuwa gare ka.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Asa kuwa ya yi kuka ga Ubangiji Allahnsa, ya ce, “Ya Ubangiji, ba wani mai taimako kamarka, wanda zai yi taimako sa'ad da mai ƙarfi zai kara da marar ƙarfi, ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama a gare ka muke dogara, da sunanka kuma muka zo don mu yi yaƙi da wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu, kada ka bar mutum ya rinjayi jama'arka.”