Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 18:32 - Littafi Mai Tsarki

32 Ya kuwa gina bagade da duwatsun da sunan Ubangiji. Ya kuma haƙa wuriya kewaye da bagaden, za ta ci kamar misalin garwar ruwa guda.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

32 Da waɗannan duwatsun ya gina bagade cikin sunan Ubangiji, ya kuma haƙa wuriya kewaye da shi, isashe da zai ci garwa biyu na irin ƙwayar gyada.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 18:32
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kome kuke yi, a game da magana ko aikatawa, ku yi duka da sunan Ubangiji Yesu, kuna gode wa Allah Uba ta wurinsa.


To, duk abin da kuke yi, ko ci, ko sha, ku yi kome saboda ɗaukakar Allah.


Sa'an nan kuma ya koma gidansa a Rama inda kuma yakan yi wa Isra'ilawa shari'a. Ya kuma gina wa Ubangiji bagade a can Rama.


Sama'ila ya kama ɗan rago ya miƙa shi ɗungum hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ya kuma yi roƙo ga Ubangiji ya taimaki Isra'ilawa, Ubangiji kuwa ya amsa addu'arsa.


Kashegari mutanen suka tashi da safe, suka gina bagade a can. Suka miƙa hadayun ƙonawa da na salama.


Sa'an nan ka gina wa Ubangiji Allahnka bagade mai kyau a kan wannan kagara. Ka ɗauki bijimi na biyu ka miƙa shi hadayar ƙonawa da itacen gumakan da za ka sare.”


Ya shirya itacen wuta, ya yanyanka bijimin gunduwa gunduwa, ya shimfiɗa shi bisa itacen. Sa'an nan ya ce a cika tuluna huɗu da ruwa, a kwarara a kan hadaya ta ƙonawar da kan itacen.


Sai Ubangiji ya bayyana ga Abram, ya ce, “Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa.” Sai ya gina bagade ga Ubangiji, wanda ya bayyana gare shi.


Gidiyon kuwa ya gina wa Ubangiji bagade a wurin, ya sa masa suna, Ubangiji Salama Ne. Har wa yau bagaden yana nan a Ofra, ta iyalin Abiyezer.


Ruwa kuwa ya malale bagaden, ya cika wuriyar da aka haƙa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ