Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 18:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Yanzu fa ka aika a tattara mini Isra'ila duka a dutsen Karmel, da annabawan Ba'al, su ɗari huɗu da hamsin, da annabawan Ashtarot kuma, su ɗari huɗu waɗanda Yezebel take kula da su.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Yanzu ka tara mutane daga dukan Isra’ila su sadu da ni a kan Dutsen Karmel. Ka kuma kawo annabawa ɗari huɗu da hamsin na Ba’al, da kuma annabawa ɗari huɗu na Ashera, waɗanda suke ci a teburin Yezebel.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 18:19
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ahab kuma ya yi gunkiyan nan Ashtoret. Ahab dai ya yi abin da ya sa Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya yi fushi fiye da dukan sarakunan Isra'ila waɗanda suka riga shi.


da Alammelek, da Amad, da Mishal. A wajen yamma, iyakar ta bi ta Karmel da Shihor-libnat.


Daga nan Elisha ya tafi har Dutsen Karmel, sa'an nan ya koma Samariya.


Sai aka kama dabbar, da kuma annabin nan na ƙarya tare da ita, wanda ya yi al'ajabai a gabanta, waɗanda da su ne ya yaudari waɗanda suka yarda a yi musu alamar dabbar nan, da kuma waɗanda suka yi wa siffarta sujada. Waɗannan biyu kuwa aka jefa su da ransu a cikin tafkin wuta da ƙibiritu.


Amma ga laifinka, wato, ka haƙurce wa matar nan Yezebel, wadda take ce da kanta annabiya, take kuma koya wa bayina, tana yaudararsu, su yi fasikanci, su kuma ci abincin da aka yi wa gumaka hadaya.


Amma fa annabawan ƙarya sun bayyana a cikin jama'a, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku, waɗanda za su saɗaɗo da maɓarnacciyar fanɗarewa, har ma su ƙi Mamallakin da ya fanso su, suna jawo wa kansu hallaka farat ɗaya.


Ko da za su hau su ɓuya a bisa ƙwanƙolin Dutsen Karmel, Zan neme su in cafko su. Ko da za su ɓuya mini a ƙarƙashin teku, Sai in sa dodon ruwa yă yayyage su.


Amos ya ce, “Ubangiji zai yi ruri daga Sihiyona, Muryarsa za ta yi tsawa daga Urushalima. Da jin wannan, sai wuraren kiwo za su bushe, Ƙwanƙolin Dutsen Karmel, da yake kore zai yi yaushi.”


Ni wanda sunana Ubangiji Mai Runduna Sarki ne, Na rantse da raina, wani zai ɓullo, Kamar Tabor a cikin tsaunuka, Ko kuwa kamar Karmel a bakin teku.


Duk da haka ba su rabu da zunuban gidan Yerobowam ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi. Sun aikata irin zunuban Yerobowam. Gunkiyan nan mai suna Ashtoret tana nan a Samariya.


Da Yehoram ya ga Yehu, sai ya ce, “Lafiya dai?” Yehu ya ce, “Ina fa lafiya, tun da karuwanci da sihirin uwarka, Yezebel, sun yi yawa haka?”


Sa'an nan Sarkin Isra'ila ya tara annabawa ɗari huɗu, ya tambaye su, ya ce, “In tafi in yi yaƙi da Ramot-gileyad, ko kuwa kada in tafi?” Su kuwa suka ce masa, “Ka haura, gama Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”


Sa'an nan ya ce wa jama'a, “Ni kaɗai ne annabin Ubangiji da ya ragu, amma annabawan Ba'al ɗari huɗu ne da hamsin.


Ya kuma fitar da tsohuwarsa Ma'aka daga zaman sarauniya, domin ta yi ƙazantacciyar siffa ta gunkiyar Ashtoret. Asa ya sassare siffar, ya ƙone ta a rafin Kidron.


Sa'an nan ya tashi tun da sassafe domin ya sadu da Saul. Aka faɗa wa Sama'ila, Saul ya tafi Karmel, ya kafa wa kansa al'amudi, sa'an nan ya juya ya wuce zuwa Gilgal.


Sai Ahab ya aika wa dukan jama'ar Isra'ila, ya tattara annabawa ɗin tare da su a dutsen Karmel.


Elisha kuwa ya ce wa Sarkin Isra'ila, “Ina ruwana da kai? Tafi wurin annabawan tsohonka da na tsohuwarka.” Amma Sarkin Isra'ila ya ce masa, “A'a, ai, Ubangiji ya kirawo mu, mu sarakunan nan uku, domin ya bashe mu a hannun Mowabawa.”


Saboda haka, yanzu sai ku kirawo mini dukan annabawan Ba'al, da dukan masu yi masa sujada, da dukan firistocinsa. Kada a manta da wani, gama ina da babbar hadayar da zan miƙa wa Ba'al. Duk wanda bai zo ba, za a kashe shi.” Amma dabara ce Yehu yake yi don ya hallaka waɗanda suke yi wa Ba'al sujada.


Duk da haka akwai Yahudawa da shugabanni ɗari da hamsin waɗanda suke cin abinci a teburina, banda waɗanda sukan zo wurinmu daga al'umman da suke kewaye da mu.


Ke kyakkyawa ce ƙaunatacciyata, Kina sa ni jin daɗi a rai.


“A cikin annabawan Samariya, Na ga abu marar kyan gani. Da sunan Ba'al suke yin annabci, Suna ɓad da jama'ata Isra'ila


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ