1 Sarakuna 18:13 - Littafi Mai Tsarki13 Ashe, ba ka ji ba? Na kasa annabawan Ubangiji biyu, na ɓoye su a kogo hamsin hamsin, sa'ad da Yezebel ta kashe annabawan Ubangiji, na ciyar da su, na kuma shayar da su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202013 Ranka yă daɗe, ashe, ba a faɗa maka abin da na yi lokacin da Yezebel ta karkashe annabawan Ubangiji ba? Yadda na ɓoye annabawa ɗari, na sa su hamsin-hamsin a kogwanni biyu, na yi ta ba su abinci da ruwa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Elisha kuwa yana zaune a gidansa, dattawa kuma suna zaune tare da shi. Sai sarki ya aiki mutum, amma kafin mutumin ya isa, sai Elisha ya ce wa dattawan, “Kun ga yadda mai kisankan nan ya aiko don a fille mini kai? Idan mutumin ya zo, sai ku rufe ƙofar, ku riƙe ta da ƙarfi. Ba da jimawa ba sarki zai bi bayansa.”