1 Sarakuna 17:12 - Littafi Mai Tsarki12 Ta ce, “Na rantse da Ubangiji Allahnka, ba ni da abinci, sai dai ɗan farin da ya ragu a tukunya, da ɗan man da yake cikin kurtu. Ga shi, ina tattara itacen don in je in shirya shi domin ni da ɗana, mu ci. Shi ke nan, ba sauran wani abu kuma, sai mutuwa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202012 Sai ta ce masa, “Na rantse da Ubangiji Allahnka, ba ni da wani abinci, sai dai ɗan gari hannu guda a tulu, da kuma ɗan mai a kwalaba. Ina tattara ’yan itacen nan ne don in kai gida in yi abinci wa kaina da ɗana, don mu ci, mu mutu.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Amma jama'a suka ce wa Saul, “Jonatan da ya yiwo babbar nasara domin Isra'ila, a ce za a kashe shi? Kai, a'a! Mun yi alkawari ga Ubangiji mai rai, Jonatan ba zai yi hasarar ko gashi guda daga kansa ba. Abin da ya yi a yau, da taimakon Allah ne ya yi.” Da haka mutane suka ceci Jonatan, har ba a kashe shi ba.